Lahadi 4 Oktoba 2026 - 19:30
Nasara da Cigaban Juyin Juya Halin Musulunci Sakamako ne na Ikhlasin Jagororin Juyin Juya Hali 

Hauza/ Mataimakan hukumar kula da makarantun Hauza na lardin Hormozgan tare da shugabannin makarantun Hauza na wannan lardi sun gana da Ayatullah Muhammad Mahdi Shabzendedar, Sakataren Majalisar Koli ta Makarantun Hauza.

A cewar rahoton Kamfanin Dillancin Labaran Hauza, Ayatullah Shabzendedar, yayin da yake nuni da yanayi na musamman na Hauzar lardin Hormozgan, ya bayyana cewa: "Kuna gudanar da ayyukanku ne a wani yanayi da yake a matsayin lardi mai gaurayayyen al'umma (mabiya mazhabobi daban-daban), kuma a halin yanzu yana cikin yanayi na yaki, kuma 'Mafi fifikon ayyuka shi ne wanda ya fi wahala' (Afdalul a'amali ahmazuha)."

Ya kara da cewa: "Allah Madaukakin Sarki ya ambata a wurare uku a cikin Alkur'ani cewa manufar halitta ita ce jarraba dan adam domin a bayyana wanne ne ya fi 'Kyawun Aiki' (Ahsanu Amala)." Ya ci gaba da cewa: "A nan akwai bahasin tafsiri kan ko ana nufin kowane aiki za a duba shi daban-daban ko 'Mafi Kyawu' ne, ko kuma ana nufin matsakaicin dukkan ayyukan mutum a tsawon rayuwarsa ya zama 'Mafi Kyawu'?"

Sakataren Majalisar Koli ta Makarantun Hauza ya kara da cewa: "Wajibi ne kowa ya sanya lamirinsa da imaninsa a kan cewa, a duk lissafi da hukunce-hukuncen da yake yi, ya mai da hankalinsa wajen ganin cewa idan aka kwatanta aikinsa da na sauran mutane, Allah Madaukakin Sarki ya ba shi lambar yabon 'Ahsanu Amala'."

Yayin da yake nuni da wani hadisi daga Imam Sadik (A.S) a cikin littafin Al-Kafi (Juzu'i na 2, shafi na 16), ya bayyana cewa: "A cikin wannan hadisi an bayyana cewa ma'aunin 'Kyawun Aiki' ba yawan aiki ba ne; a'a, ma'aunin shi ne yadda aikin ya dace da kyawawan dabi'u da manufofi na kwarai."

Ya bayyana "Khashyatu Lillahi" (Tsoron Allah da kankan da kai a gabansa) a matsayin rukuni na farko na samun 'Kyawun Aiki' a cikin hadisin, tare da bayyana banbanci tsakanin "Khawf" da "Khashyah": "Khawf yana nufin tsoro, wato mutum yana tsoron kada a lokacin hisabin ayyukansa ya zama dan wuta, kuma tabbas wannan tsoron ma abin so ne; amma Khashyah tana samo asali ne daga zurfin ma'arifa da sanin Allah Madaukaki, kuma sakamakon wannan babban sani ne mutum yake samun kaskantar da kai a gaban girman Ubangiji, koda kuwa ma'asumi ne wanda ba ya aikata wani zunubi ko kadan."

Wannan babban malami na Hauzar Ilmi ta birnin Qum ya bayyana "Kyakkyawar Niyya domin neman kusanci ga Allah" a matsayin rukuni na biyu, yana mai jaddada cewa: "Saboda haka, idan shugaba yana da Khashyar Ubangiji, to dukkan ayyukansa da hukunce-hukuncensa za su ginu ne a kan wannan tushe mai muhimmanci."

Da yake jawabi ga malaman makarantun Hauza, ya bayyana cewa: "Idan malami yana son ya kasance mai 'Ahsanu Amala', dole ne ya kasance mai tausayi da damuwa ga dalibai, ya yi bincike da karatu sosai, ya isar da darussa cikin kyakkyawan tsari, ya kasance mai kiyaye tsari da zuwa a kan lokaci, kuma ya kasance ma'abucin ruhi da kyawawan dabi'u."

Wannan mamba na Kungiyar Malaman Hauzar Qum, yayin da yake kafa misalai da tarihin manyan malamai da magabata na Hauza wajen tarbiyya da tsarkake kai, ya ce: "Idan malami ya kasance ma'abucin ruhi da takawa, dalibi zai fahimci karatu sosai kuma zai amfana da ruhin malamin."

A wani bangare na jawabinsa, yayin da ya yi magana game da marigayi Aytullahil Uzma Sayyid Musa Shubairi Zanjani, ya bayyana zurfin binciken ilimi da kuma kankan da kai a matsayin siffofi na musamman na wannan marja'i, tare da bayyana rasuwarsa a matsayin wani babban gibi da rashi ga al'umma.

Ayatullah Shabzendedar ya bayyana cewa daya daga cikin manyan siffofin Jagoran Juyin Juya Hali Shahidi, kamar yadda yake ga Imam Khumaini (Rahamar Allah ta tabbata a gare su), shi ne tsarkakakkiyar ikhlasi, kuma ya alakanta nasarar Juyin Juya Halin Musulunci da wannan ikhlasi, inda ya ce: "Wannan ikhlasi ya samu wannan albarka har Juyin Juya Halin Musulunci ya yi nasara kuma ya tsaya tsayin daka a gaban dukkan matsalolin da makiya suka haifar."

Alamomi

Ra'ayinka

You are replying to: .
captcha